logo

HAUSA

Kumbon Shenzhou-17 ya rabu da turkensa na tashar binciken samaniya

2024-04-30 10:20:53 CMG Hausa

Hukumar lura da binciken sararin samaniya ta Sin, ta ce kumbon Shenzhou-17 mai dauke da ’yan sama jannati, ya rabu da turkensa na tashar binciken samaniya mallakin kasar Sin a yau Talata.

Kumbon dauke da ’yan sama jannati Tang Hongbo, da Tang Shengjie da Jiang Xinlin, na shirye-shiryen dawowa doron duniya nan gaba a Talatar nan.   (Saminu Alhassan)