logo

HAUSA

Sin ta mai da martani kan matakin kayyade yawan kayan laturoni masu amfani da “Semiconductors” da Japan ke fitarwa ketare

2024-04-29 15:16:04 CMG Hausa

 

Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin kasar Sin, ya ce an gano yadda gwamnatin Japan ta yi shirin kayyade yawan kayan laturoni masu amfani da “Semiconductor”, da sauran kayayyaki masu alaka da Japan ke fitarwa ketare, kuma Sin na matukar bayyana rashi jin dadi kan hakan.

Jami’in ya ce, Sin na kalubalantar Japan, da ta dakatar da wannan kuskure mai nasaba da cinikayyar bangarorin biyu, ta yadda za a ba da tabbaci ga tsarin samarwa, da jigilar hajoji a duniya, yayin da a nata bangare Sin za ta dauki matakan da suka wajaba, don kiyaye moriyar kamfanoninta.

Mai magana da yawun ma’aikatar ya yi wannan furuci ne a yau Litinin, bayan da a ranar 26 ga watan nan, gwamnatin Japan ta saurari ra’ayin jama’arta, game da shirinta na gudanar da shirin kayyade wasu bangarorin dake da nasaba da kayan laturoni, masu amfani da “Semiconductor” da take fitarwa ketare. (Amina Xu)