Hamas: Ba za a cimma yarjejeniya da Isra’ila ba muddin ana ci gaba da yaki a Gaza
2024-04-29 11:27:02 CMG Hausa
Kungiyar Hamas ta Palasdinu, ta bayyana a jiya cewa, ba za ta aminice da wata yarjejeniya da Isra’ila ba, muddin ba ta kunshi dakatar da bude wuta a zirin Gaza ba.
Wata sanarwa da kungiyar ta fitar jiya, ta ruwaito Sami Abu Zuhri, wani babban jami’inta na cewa, ba za su amince da yarjejeniyar da ba ta kunshi dakatar da bude wuta a Gaza ba. Inda ya kara da cewa, suna nazarin martanin Isra’ila, wanda ya isa ga Hamas din ta hannu masu shiga tsakani, yana mai cewa, ya yi wuri su cimma matsaya kansa.
Rahotanni daga kamfanin dillancin labarai na WAFA na Palasdinu, sun ce wasu luguden wuta 3 da Isra’ila ta kai kan gine-ginen wasu unguwanni a birnin Rafah dake kudancin zirin Gaza, ya yi sanadin mutuwar akalla Palasdinawa 15 a daren ranar Lahadi
Haka kuma, wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wasu mutane da dama kuma sun makale karkashin baraguzai, inda ma’aikatan tsaron al’umma ke aikin ceto su. (Fa’iza Mustapha)