logo

HAUSA

Hukumar sadarwa ta CSC ta Burkina Faso ta dakatar da watsa shirye-shiryen wasu kafofin sadarwa

2024-04-29 10:55:54 CMG Hausa

Bayan wani zaman taronta, a ranar jiya Lahadi 28 ga watan da muke ciki, hukumar sadarwa ta CSC ta kasar Burkina Faso ta gano wani labarin da aka watsa a ranar Asabar 27 ga watan Afrilun shekarar 2024, bisa gidajen rediyo da na shafukan sada zumunta na TV5, DW, OUEST-FRANCE, LE MONDE.FR, ApaNews, The Gardian da Agence Ecofin, da wani rahoton bidiyo da wani sharhin da ke zargin rundunar sojojin Burkina Faso da kashe fararen hula a arewaci da kuma arewa maso gabashin kasar.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.  

Wadannan zarge-zarge sun biyo bayan wani rahoto na kungiyar Human Rights Watch kan shafinta na yanar gizo. Hukumar sadarwa ta CSC ta gano cikin wannan rahoto da aka watsa bisa kafofin sadarwa daban daban, da bayanai na neman fitina da son kai kan rundunar sojojin Burkina Faso. Lamarin da ya sha bamban da girmama sharudan aikin jarida bisa tattara da tace labari da ma tabbatar da sahihancinsa kafin a watsa shi. Wannan na nuna cewa an yi amfani da labarun karya domin bata sunan rundunar sojojin Burkina Faso. Haka kuma, baya ga wannan hanya ta tace labari mai hadari da ya shafi sojojin Burkina Faso dake iyar janyo tashin hankali da gurbata zaman jituwa da aya mai lamba 130 ta doka mai lamba 058-2015/CNT ta ranar 4 ga watan Satumban shekarar 2015 da ta shafi halin shari'a na watsa labarun rediyo da na talabijin a kasar Burkina Faso ke hukuntawa.

Bisa ga sakamakon haka ne da kuma la'akari da hadarin da ke tattare da wannan al'amari, zauren mashawarta na hukumar sadarwa ta CSC, bayan taron gaggawa ya yanke shawara kamar yadda dokoki suka tanada na dakatar da watsa shirye-shiryen TV5 a Burkina Faso bisa tsawon sati 2 da kuma dakatar da hanyoyin samun TV5, DW, OUEST France, Le Monde.fr, ApaNews, Thé Gardian da kuma Agence Ecofin a kan shafukan sada zumunta daga kasar Burkina Faso har zuwa wani sabon lokaci.

Daga karshe kuma hukumar sadarwa ta CSC ta yi kashedi ga dukkan kafafen yada labaru da su guji yada irin wadannan labaru, idan suka sabawa doka, to doka za ta yi aikinta.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.