logo

HAUSA

Ma Fan: kokarin kara fahimtar ilmin likitancin gargajiyar kasar Sin a Faransa

2024-04-29 16:05:50 CMG Hausa


Ma Fan, shugabar cibiyar nazarin ilmin likitancin gargajiyar kasar Sin ta Shaoyang, ko da yaushe tana dukufa wajen yada ilmin likitancin gargajiyar, da kuma koya wa Turawa ilimin, tun bayan da ta zauna a kasar Faransa a shekarar 1992. A cikin shekaru da dama da suka gabata, ta gudanar da laccoci kan ilmin likitancin gargajiyar Sin da al'adun kasar a kasashen Turai.

An haifi Ma Fan a yankin Liangshan ta kabilar Yi mai cin gashin kansa na lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, a shekarar 1964. Kakanta da iyayenta duk malamai ne.

Ma Fan ta samu digiri na farko a kwalejin likitanci ta Luzhou da ke birnin Luzhou na lardin Sichuan, sannan ta yi digiri na biyu a jami'ar likitancin gargajiyar Sin ta birnin Chengdu, hedkwatar lardin Sichuan.

Yayin da take zaune a Chengdu, Ma Fan ta kan kai abokan karatunta na kasashen waje zagayawa cikin birni don sayen abin da suke bukata, da kuma yin qigong, wani nau’in wasan motsa jiki na numfashi na kasar Sin, da kuma wasan Kongfu na kasar Sin, irin su tai chi. Yayin da take karatu a jami'ar likitancin gargajiyar Sin ta birnin Chengdu, Ma Fan ta hadu da wani dalibi dan kasar Faransa, kuma ta kamu da soyayyarsa, wanda daga bisani ya zama mijinta.

Bayan ta kammala karatu, Ma Fan ta bar aikin da take yi a Chengdu, ta bi masoyinta zuwa Montpellier, wurin yawon bude ido a kudancin Faransa. A farkon lokacin da ta isa Montpellier, Ma Fan ta fuskanci kalubale da koma baya, wadanda matsalolin rashin jin yare suka haifar da kuma rashin samun aikin yi bisa kwarewarta ta likitancin gargajiyar Sin.

Tare da goyon bayan mijinta, Ma Fan ta yi iya kokarinta don inganta iya amfani da harshen Faransanci, kuma ta ci gaba da aika da bayanin aikinta da fatan samun aikin da ya shafi likitancin gargajiyar Sin. A wancan lokacin, ba a san likitancin gargajiyar Sin ba, ko kuma ba a tallata shi a Faransa ba. Yawancin mutanen Faransa ba su san komai game da likitancin gargajiyar Sin ba.

Bayan watanni da dama, Ma Fan ta samu wata damar aikin daga makarantar likitancin gargajiyar Sin a arewacin Faransa. Ta karbi damar duk da cewa dalibai biyu ne kawai ta samu kuma ba za a biya ta albashi ba.

Wannan aikin da ta samu ya sa Ma Fan ta inganta Faransancinta, ta fahimci tsarin ci gaban likitancin gargajiyar Sin a Faransa, kuma ta dawo da kwarin gwiwarta.

Sannu a hankali, Ma Fan ta bullo da wani tsari mai ma’ana game da aikinta a Faransa, wanda ta fara ta hanyar bude nata asibitin likitancin gargajiyar Sin. Da farko, Ma ta kafa dan karamin dakin karbar jinya, mai gadon da mijinta ya hada, domin ba ta da kudin hayar gida. Duk da cewa Faransawan sun zakku su fahimci yadda tsarin likitancin gargajiyar Sin yake, amma sun sa ido su ga yadda asibitin Ma zai kankama.

Wani bafaransa, direban babbar mota wanda ke fama da ciwon baya ne majinyacinta na farko. Ba da jinya ta hanyar tsira allura a jikin mutum wato Acupuncture na gargajiya na kasar Sin ya haifar da sakamako mai ban mamaki. Don nuna godiya, mutumin ya aikawa Ma Fan sabon gadon tausa, kuma ya taimaka mata tallata asibitin.

Tun daga wannan lokacin, Ma Fan da asibitinta sun shahara. Sau da yawa ta kan yi tafiya a fadin kasar Faransa, da sauran kasashen Turai, don ba da laccoci kyauta game da likitancin gargajiyar Sin, don tallata al'adun a Turai.

A karshe, Ma Fan ta yanke shawarar kafa makarantar likitancin gargajiyar Sin, saboda ta fahimci cewa, ba abu mai sauki ba ne ta tsara tsarin koyar da ilimin likitancin ga mutanen yankin ta hanyar laccoci, wanda ke daukar awa biyu ko uku a kowace lacca.

A shekarar 1995, 'yan matan Switzerland biyu sun ziyarci asibitin Ma Fan, kuma sun ce suna son koyon ilmin likitancin gargajiyar Sin. Yayin da suke karatu a asibitin, sun shawarci Ma Fan ta bude makarantar koyar da ilmin likitancin a Switzerland. Shawarar tasu ta yi daidai da tunanin Ma Fan na bude makaranta.

Tare da goyon bayan wani dan Swiss, Ma Fan ta samu amincewa ta bude makarantar a birnin Lausanne. Sai dai ba abu mai sauki ba ne dalibai su so shiga makarantar da ba ta riga ta yi suna ba.

Da farko dai, makarantar tana da dalibai biyar ne kacal, wadanda tsofaffin daliban Ma Fan suka ba su shawarar shiga makarantar. Kudin da Ma Fan ta samu ya gaza biyan bukatun makarantar. Duk da haka, Ma Fan ta dage da bin burinta.

Abin mamaki, makarantarta ta dauki hankalin kafafen yada labarai na Lausanne. A cikin 1997, wata jarida a Switzerland ta wallafa wani rahoto mai zurfi game da makarantar koyar da ilmin likitancin gargajiyar Sin ta Ma Fan, sakamakon hakan ya sanya mutane da yawa suka nemi izinin shiga makarantar.

Nasarar da makarantar ta samu ta karawa Ma Fan kwarin gwiwa, kuma ta karfafa mata gwiwa ta bude cibiyar koyar da ilmin likitancin gargajiyar Sin ta kasa da kasa ta Shaoyang, a birnin Lyon na Faransa, a shekarar 1998. Tun daga wannan lokacin, Ma Fan take zirga-zirga tsakanin Faransa da Switzerland don gudanar da aikinta.

A shekarun da suka gabata, dubban Turawa sun bi Ma Fan, don koyon ilmin likitancin. Ma Fan ta bayyana cewa, "mafi yawansu Faransawa ne. Wasu suna nazarin ilmin likitancin saboda sha'awa, wasu kuma a matsayin aikin yi, amma dukkansu na da kamanceceniya daya wato kaunar ilmin likitancin gargajiyar Sin, kuma cike da sha'awar al'adun Sinawa."  

Wasu daga cikin daliban Ma Fan sun ziyarci kasar Sin don zurfafa karatunsu na ilmin likitancin gargajiyar Sin. Wasu kuma sun kafa nasu asibitoci da makarantu, sun zama kashin bayan ci gaban ilmin likitancin a Faransa.

Cibiyar koyar da ilmin likitancin gargajiyar Sin ta kasa da kasa ta Shaoyang ta zama wani muhimmin dandali wajen raya ilmin a Turai, da kuma inganta mu'amalar al'adu da jama'a tsakanin Sin da Faransa.

A shekarar 2004, an zabi Ma Fan a matsayin shugabar kungiyar likitancin gargajiyar Sin ta kasar Faransa, bisa la'akari da irin gagarumar gudunmawar da ta bayar ga ci gaban ilmin likitancin a Faransa da sauran kasashen Turai.

Duk lokacin da Ma Fan ta tuna da yadda mutanen Turai masu dimbin yawa ke sha'awar koyon ilmin likitancin gargajiyar Sin da al'adun Sinawa, ta kan yi farin ciki sosai. Ta kan ce ta yi sa'a ta karanci likitancin gargajiyar Sin.

Kazalika, Ma Fan ta mai da hankali sosai kan ci gaban garinsu na Liangshan, kuma ta tallafa wa ayyukan walwalar jama'a daban-daban na wurin.

A shekarar 2022, Ma Fan ta koma kasar Sin ta ziyarci garinsu na Liangshan. Manyan sauye-sauyen da aka yi a garinsu sun burge ta sosai. Ta yi fatan ta zama wata alakar hada kan kamfanonin Liangshan da takwarorinsu na ketare wajen gudanar da mu'amala da hadin gwiwa da samun ci gaba tare.

Ma Fan ta ce, “ilmin likitancin gargajiyar Sin ne ta sanya rayuwata ta canza, wanda ya ba ni damar ficewa daga garinmu na shiga cikin duniya mai fadi. Zan ci gaba da dagewa wajen habaka fahimtar al'adun likitancin gargajiyar Sin a Turai, da inganta mu'amalar al'adu tsakanin Sin da Faransa ta hanyar samun ci gaban ilmin likitancin."(Kande Gao)