Taron musamman na dandalin tattalin arzikin duniya ya yi kira da a kara hadin kai tsakanin kasa da kasa
2024-04-29 11:35:34 CMG Hausa
An gudanar da taron musamman na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya wato WEF a jiya Lahadi a birnin Riyadh, hedkwatar kasar Saudiyya, inda aka mai da hankali matuka kan hadin kan kasa da kasa da samun bunkasuwa da makamashi. Kana an tattauna kan yadda za a shimfida yanayi mafi inganci na bunkasa tattalin arzikin duniya ta hanyar kara azamar hadin kan kasa da kasa.
Babban darektan dandalin Borge Brende ya bayyana a cikin jawabinsa na bude taron cewa, ana tsananin bukatar hadin kai da mu’ammala tsakanin kasashe daban-daban a halin yanzu, saboda halin da ake ciki a wasu sassa na kara tsananta da kara gibin tattalin arziki tsakanin al’umma, abubuwan dake haifar da bambancin ra’ayi tsakanin kasa da kasa. Duba da hakan, taron a wannan karo na samar da wani zarafi mai yakini ga shugabannin sana’o’i da na sassan duniya, ta yadda za su tattauna kan manufofin tinkarar kalubaloli.
A nata bangare, shugabar asusun ba da lamuni na duniya IMF Kristalina Georgieva ta yi kira ga kasa da kasa da su magance matsalar basusuka ta hanya mai dorewa. A cewarta, kamata ya yi Amurka ta duba matsalarta na karuwar basusukan da take da su, da kuma sauke nauyin dake wuyanta yadda ya kamata. Ban da wannan kuma, ta ce, ya kamata a ingiza ciniki tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a samu karuwar amfani da kudade. (Amina Xu)