logo

HAUSA

Philippines ba ta da imani ko kadan

2024-04-29 14:03:05 CMG Hausa

Ministan tsaron kasar Philippines, Gilberto Teodoro ya bayyana a shekaranjiya 27 ga wata cewa, tun da gwamnatin kasar mai ci ta hau karagar mulki a shekara ta 2022, kawo yanzu, ma’aikatar tsaron kasar ba ta da masaniya, kana, ba ta taba cimma wata yarjejeniya da kasar Sin, game da rikicinsu kan tekun kudancin kasar Sin ba. Wannan ya shaida cewa, Philippines ta sake musunta yarjejeniyar da ta cimma da kasar Sin kan batun karamin tsibirin Ren’ai Jiao, baya ga musuntawar da shugaban kasar, Ferdinand Marcos, da mashawarcinsa kan harkokin tsaron kasa, Eduardo Ano suka yi.

Domin tabbatar da halin karko da ake ciki a tekun kudancin kasar Sin, kasashen Sin da Philippines sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya dangane da batun karamin tsibirin Ren’ai Jiao, a yayin mulkin gwamnatin Rodrigo Duterte. Bisa yarjejeniyar, Philippines ta alkawarta cewa, ba za ta ci gaba da kaiwa jiragen ruwan sojan da ta jibge a can kayayyakin gine-gine ba. Sai dai kuma bisa ra’ayin nuna jin-kai, kasar Sin ta amince da matakin Philippines na kaiwa sojojin jiragen ruwan kayan rayuwa na wani gajeren lokaci. Tun da gwamnati mai ci ta hau karagar mulki a watan Yunin shekara ta 2022 har zuwa watan Fabrairun shekara ta 2023, hukumomin kasashen Sin da Philippines sun kiyaye wannan yarjejeniya, kaza lika, kasar Sin ta gabatar da bayanai sau da dama da suka shafi yarjejeniyar ga manyan jami’an Philippines.

Amma manyan jami’an Philippines na gwamnati mai ci sun ce ba su da masaniya ko kadan game da yarjejeniyar da gwamnatin da ta shude ta cimma da kasar Sin, sun sani amma sun take sani. Dalilin gwamnatin Philippines na cin amana gami da kaiwa jiragen ruwan sojan da ta jibge ba bisa doka ba kayayyakin gine-gine shi ne, tana yunkurin samun tallafin kasar Amurka, da neman inganta karfin sojanta na ruwa, da cimma burin mamaye karamin tsibirin Ren’ai Jiao har abada. A don haka, har ta zama wata kafa da Amurka take amfani da ita wajen yin shisshigi cikin harkokin shiyyar.

Wasu matakan da Amurka ta dauka, na tsallake jan layi, da girke makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango a Philippines, za su kara ta’azzara halin da ake ciki a yankin. Hakikanin gaskiya, wadannan abubuwan da Philippines ta yi, tamkar kai kanta ne ga hallaka. Kaza lika, musunta yarjejeniyar da ta yi, zai sa kasar ta zama mai aikata laifi, dake musunta tarihi, da cin amana, gami da haifar da rudani ga halin da ake ciki a shiyyar. (Murtala Zhang)