logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Isra’ila: Za a iya dakatar da kai hari Rafah idan an cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta

2024-04-28 15:54:58 CMG Hausa

 

Ministan harkokin wajen kasar Isra’ila Israel Katz, ya bayyana a jiya Asabar cewa, idan kasarsa ta cimma matsaya da kungiyar Hamas ta Palasdinu, kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, sojin Isara’ila za su dakatar da kaiwa birnin Rafah dake kudancin Gaza hare-hare ta kasa.

Israel Katz, ya bayyana hakan ne ga manema labarai ta tasha ta 12 ta gidan talibijin na Isra’ila, inda ya kara da cewa, aikin dake kan gaba shi ne sako ’yan Isra’ila da aka tsare a Gaza.

Bisa labarin da tashar ta bayar a jiya, tawagar kasar Masar ta yi shawarwari da bangaren Isra’ila a ranar Juma’a, kuma Isra’ila ta isarwa Hamas bukatunta ta bakin Masar game da yarjejeniyar, kuna a cewarta, wannan shi ne zarafi na karshe, don gane da kulla yarjejeniya, kafin kasar ta kai hari ta kasa a Rafah.

A nata bangare, Hamas ta fitar da wata sanarwa da safiyar jiya, inda ta ce ta samu martanin Isra’ila game da batun kulla yarjejeniya, kuma yanzu haka ana ci gaba da tattauna kan lamarin. (Amina Xu)