An wallafa littafi game da bayanan Xi don gane da shawarar BRI na harshen Turanci
2024-04-28 21:28:16 CMG Hausa
Madaba’ar tattara bayanai da fassara ta kasar Sin, ta wallafa littafi game da bayanan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi don gane da shawarar ziri daya da hanya daya ko BRI, bugun harshen Turanci na shekarar 2023.
Wata sanarwar hukuma da aka fitar a Lahadin nan, ta ce za a rarraba littafin a sassan cikin kasar Sin da ma kasashen waje.
Sanarwar ta kara da cewa, ana fatan wallafar za ta taimakawa masu karatu na kasashen ketare, da damar kara fahimtar ma’ana, da matakai, da manufofi, da nasarorin da shawarar BRI ta cimma, kana hakan zai taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa hadin gwiwar kasa da kasa karkashin shawarar ta BRI. (Saminu Alhassan)