logo

HAUSA

Gwamnatin kasar Qatar ta kaddamar da shirin taimakawa marayu 1000 a jihar Borno

2024-04-28 09:38:32 CMG Hausa

Gwamnatin kasar ta kaddamar da shirin taimakawa marayu dubu daya a jihar Borno

Jakadan kasar Qatatr a Najeriya Dr. Ali Bin Ghanem Al-Hajari ne ya tabbatar da hakan a ranar 27 ga wata a garin Maiduguri, yayin aza harsashin ginin makarantar firamare ta marayu a birnin a matsayin matakin farko na cimma burin da aka sanya a gaba.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana rahoto.

 

Jakadan na kasar Qatar a Najeriya ya ce, gwamnatin kasar za ta samar da tallafin kayayyakin bukatu ga marayu dubu daya, inda ya ce, kaddamar da ginin sabuwar makarantar firamaren yana daya daga matakai na samar da kyakkyawan yanayin karatu ga irin wadannan marayu, baya ga wannan kuma za a dauki nauyin karatun wasu yaran.

Ya ce, gwamnatin kasar ta Qatar ta tsara aiwatar da jerin ayyukan jin kai guda 8 a harabar cibiyar bunkasa ilimin addinin musulunci dake Maiduguri, inda a wannan waje ne ake aikin gina makarantar firamaren.

A lokacin da yake jawabi, darkatan gidauniyar bayar da agaji ta kasar Qatar Sheik Hamdin bin Abdul ya kara bayanin cewa,

“A cikin mako mai kamawa za mu fara aikin ginin gidaje domin ma’aikata, a gaba kuma za mu yi kokarin gina masallaci, da asibiti da kuma shaguna sai sauran ayyuka kuma su biyo baya sannu a hankali.”

A jawabinsa, gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum godiyarsa ya mika ga gwamnatin kasar ta Qatar saboda yadda take nuna tausayawa ga yara marayu dake jihar ta Borno.

“Ina tabbatar maku cewa gwamantin jihar Borno za ta goyi bayan dukkan wasu shirye-shirye da gidauniyar kasar Qatar ta bijro da su wadanda za su kawo sauki ga al’ummar jihar Borno”. (Garba Abdullahi Bagwai)