logo

HAUSA

Wang Yi ya zanta da mai ba da shawara kan harkokin waje ga shugaban kasar Faransa

2024-04-28 15:13:09 CMG Hausa

 

A jiya Asaba, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana darektan ofishin harkokin wajen kwamitin kolin jam’iyyar, Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho, da mai ba da shawara kan harkokin waje ga shugaban kasar Faransa Emmanuel Bonne.

Yayin zantawar tasu, Wang Yi ya ce, Sin da Faransa na nacewa matsayin ’yancin kai, da dogaro da kanta, da hadin kai, da cin moriya tare, kuma suna adawa da haifar da baraka tsakanin sassan duniya, da nuna kiyayya tsakanin bangarori daban-daban, kana suna tsayawa tsayin daka kan gudanar da cudanyar bangarori daban-daban, da kiyaye tsarin mulkin MDD da dokar kasa da kasa.

Ya ce Sin na fatan kara tuntuba tsakanin shugabannin kasashen biyu, ta yadda za su ba da jagoranci ga ayyukan diplomasiyya, da habaka ma’anar huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu. Daga nan sai ya yi fatan Faransa za ta ci gaba da gaggauta kungiyar tarayyar kasashen Turai wato EU, a fannin daukar matakan da suka dace game da kasar Sin.

A nasa bangare, Emmanuel Bonne ya ce, Faransa na fatan kara azamar tuntubar shugabannin kasashen biyu, bisa muhimmin lokaci na cika shekaru 60 da kafuwar huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, da ma zurfafa amincewar juna, da kara hadin kai da cin moriyar tare. A cewarsa, ya kamata kasashen biyu su kara hadin gwiwa don kwantar da hankali a wasu yankunan da suka fi jawo hankali, da tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta baki daya, ciki har da sauyin yanayi.

Ban da wannan kuma, ya kamata su ba da gudunmawarsu a fannin rage gibin dake tsakanin kasashe masu wadata da kasashe masu tasowa, da kauracewa gaba da juna tsakanin bangarori daban-daban, da gaggauta bunkasuwar huldar Faransa da Sin, da ma kasashen Turai da Sin. (Amina Xu)