logo

HAUSA

Dan Nijar Evann Abba Girault ya samu tikitinsa na wasannin Olympic na Paris a wasan takobi na Escrime

2024-04-28 10:18:02 CMG Hausa

A ranar jiya Jumma’a 27 ga watan Afrilun shekarar 2024, dan kasar Nijar Evann Abba Girault ya samu tikitinsa na wasannin Olympic na Paris bayan ya doke dan kasar Aljeriya Zacharia a wasan fidda gwani na wasan takobi na Escrime da ya gudana a birnin Alger.

Daga birnin Yamai abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.  

A karon farko ne kuma a cikin tarihin irin wannan wasan takobi na Escrime wani dan kasar Nijar cewa da Evann Abba Girault ya fafata wasan wucewa gaba a wasan takobi na Escrime a ranar jiya da misalin karfe 5 da mintoci 55 na yamma a birnin Alger na kasar Aljeriya. Dan kasar Nijar ya lashe abokin wasansa na kasar Aljeriya Zacharia da suka 15 da 10. Nasarar da ta baiwa Evann Abba damar wucewa gaba da makin ban girma na halarta wasannin Olympic da za su gudana a birnin Paris na kasar Faransa daga ranar 26 ga watan Yuli zuwa ranar 11 ga watan Augustan shekarar 2024.

A halin yanzu, bayan Alfaga da Noureddine Issaka a wasan motsa jiki na Taekwondo, Evann Abba Girault ya zama dan Nijar na uku da ya samu tikitin halartar wasannin kasa da kasa na Olympic na birnin Paris.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyarn Nijar.