logo

HAUSA

Manoman citta a jihar Kaduna sun bayyana fargabar sake tafka asara sakamakon bullar wata cuta dake cinye amfani

2024-04-27 16:15:05 CMG Hausa

Wata cuta dake lalata kwayar citta ta sake bulla a jihar Kaduna dake arewacin Najeriya, lamarin da ka iya haifar da karancin citta a bana a kasar.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis 25 ga wata, janaral manajan hukumar bunkasa ayyukan gona na jihar Alhaji Mohammad Rili, ya ce an taba samun bullar wannan cuta a bara inda manoma suka yi asarar a kalla naira biliyan 10.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Jihar Kaduna na daya daga cikin yankunan da suke samar da kaso mafi yawa na citta a duniya, inda kamar yadda bincike ya nuna ana samar da kaso 18 a duk shekara na adadin cittar da ake bukata a duniya.

A cewar janaral Manajan hukumar bunkasa aikin gona na jihar Kaduna, sake bullar wannan cuta za ta haifar da wani mummunan koma baya a sha’anin noma citta a Najeriya.

Ya ce babban kalubalen da ake fuskanta shi ne na karancin irin shuka, ya ce babu wanda yake shigo da irin shuka na citta kasar nan kamar yadda ake shigo da irin shinkafa ko masara, kuma muddin wannan cuta ta ci gaba, za a iya kaiwa ga gabar da noman citta zai gagara a Najeriya.

Alh Muhammad Rili wanda ya yabawa gwamnatin tarayya sabo da tallafin naira biliyan daya da dubu dari 6 da ta bayar domin rabawa  manoman cittar da suka yi asara a shekara ta 2023, duk da cewa mutane na kokawa kan gaza baiwa manoma na hakika tallafin, amma ya ce yanzu gwamnatin jihar ta Kaduna ta dauki matakai domin ganin manoma na hakika ne kawai za su rinka amfana da duk wani tallafin gwamnati.

“Muna kan aikin samar da wata mahaja da za ta kai mu zuwa ga mataki na gaba wadda ya kunshi cikakkun bayanan kowanne manomi a inda a duk lokacin da muke neman manoman masara kawai za mu shiga mahajar ne kai tsaye ya kai mu, haka su ma manoma shinkafa da su kansu manoma citta, wannan tsari hakika zai yi mana maganin manoman bogi”. (Garba Abdullahi Bagwai)