Shugaban kasar Suriname: Tunanin shugaba Xi Jinping ya samar da sabuwar hanyar bunkasa duniya
2024-04-27 16:16:34 CMG Hausa
A kwanakin baya, shugaban kasar Suriname Chandrikapersad Santokhi ya bayyana wa wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG cewa, kiran bunkasa duniya, da kiran kiyaye tsaron duniya, da kuma kiran kiyaye al’adun duniya, dukkansu sun shaida hangen nesa da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi.
Shugaba Santokhi ya ziyarci dakin nune-nunen tarihin jam’iyyar Kwaminis ta Sin, inda ya nuna yabo ga tarihin Sin, da bunkasuwar Sin, da kokarin jama’ar kasar Sin, da kuma kokarin da aka yi wajen kafa wata kasa mai ‘yancin kai dake da mutane fiye da biliyan 1.
Shugaba Santokhi ya yi nuni da cewa, shugaba Xi Jinping ya samar da sabuwar hanyar bunkasa duniya, wanda ya gabatar da kiran bunkasa duniya, da yin kokarin yaki da talauci, da gabatar da kiran kiyaye tsaron duniya da shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya, don sa kaimi ga samun wadata da kara yin hadin gwiwa da juna a duniya da kuma fadada zuba jari a yankuna daban daban. A ganinsa, tunanin shugaba Xi Jinping ya samu nasara, karin kasashen duniya za su bi hanyar samun bunkasuwa bisa tunanin shugaba Xi. (Zainab Zhang)