logo

HAUSA

WHO: Liberia, Benin, da Saliyo sun kaddamar da allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro

2024-04-27 16:37:19 CMG Hausa

 

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa, kasashen Liberia, Benin da Saliyo sun kaddamar da allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro, wadda zai shafi miliyoyin kananan yara a wadannan kasashen uku na yammacin Afirka.

A cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu a ranar Juma’a a birnin Monrovia, babban birnin kasar Liberia, WHO ta bayyana cewa, kaddamar da allurar rigakafin a ranar cutar zazzabin cizon sauro ta duniya, wadda ake murnar ta a ranar 25 ga watan Afrilun kowace shekara, zai taimaka wajen kara yi wa mutane allurar rigakafin a nahiyar Afirka.

Sanarwar ta kara da cewa, "Kaddamar da shirin na yau ya kara adadin kasashe zuwa takwas a nahiyar Afirka, wadanda ke shigar da yin allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro cikin shirye-shiryen rigakafin yara, wanda zai ba da damar samun cikakkiyar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro," 

Kasashe sama da 30 na Afirka sun nuna sha'awarsu ga allurar, ciki had da wasu sun shirya kaddamar da allurar a shekarar 2025, a cewar WHO.

Kasar Ghana na da burin rage mutuwar mutane masu fama da cutar zazzabin cizon sauro da kashi 90 cikin kashi 100 nan da shekarar 2028, a cewar wani jami'in kasar. Mataimakin manajan shirin kawar da cutar zazzabin cizon sauro na kasar Ghana Nana Yaw Peprah, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kasarsa za ta fara baiwa jama’a magunguna a wasu gundumomi da aka zaba domin kula da duk masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro cikin lokaci. (Yahaya)