logo

HAUSA

Amurka za ta janye sojoji daga Chadi da Nijer

2024-04-27 16:49:21 CMG Hausa

Shugaban taron hafsoshin sojojin kasar Amurka Charles Quinton Brown ya tabbatar a jiya cewa, Amurka za ta janye yawancin sojanta daga kasashen Chadi da Nijer.

Brown ya bayyana a gun taron manema labaru da ma’aikatar tsaron kasar ta gudanar a wannan rana cewa, wannan kuduri ne da sojojin Amurka suka tsai da bisa canjin yanayin da ake ciki a wurin. Amma sojojin Amurka za su ci gaba da aiwatar da ayyukan yaki da ta’addanci a nahiyar Afirka, da yin hadin gwiwa da kasashen Afirka, don kiyaye mutuncinsu a nahiyar ta Afirka.

Jaridar The New York Times ta hakaito labarin da jami’in Amurka ya bayar cewa, Amurka na shirin janye sojojin kasa na musamman kimanin 75 daga Chadi, da kuma sojoji fiye da 1000 daga Nijer.

An ruwaito cewa, a farkon wannan wata, bangaren sojan Chadi ya bukaci sojojin Amurka su janye daga sansanin sojan sama na Aigecosai dake dab da birnin N'Djamena, babban birnin Chadi bisa dalilin cewa, sojojin Amurka ba su samu izni ba. A watan Maris na bana, gwamnatin Nijer ta sanar da soke yarjejeniyar hadin gwiwar soja da Amurka, tare da bukatar Amurka ta janye sojanta daga Nijer. (Zainab)