logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Gudanar Da Bincike Kan Fashewar Bututun Iskar Gas Na Nord Stream Karkashin Jagorancin MDD

2024-04-27 16:24:56 CMG Hausa

Wakilin kasar Sin a ranar Juma'a ya yi kira da a gudanar da binciken kasa da kasa karkashin jagorancin MDD game da fashewar bututun iskar gas na Nord Stream a watan Satumban shekarar 2022.

An shafe fiye da watanni 18 tun faruwar lamarin. Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang ya ce, abin takaici ne cewa ba a cimma matsaya ba.

Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin ta lura da cewa, kasashen Sweden da Denmark, manyan bangarorin biyu da ke cikin lamarin, sun sanar a watan Fabrairun shekarar 2024, da kawo karshen bincikensu na musamman. Binciken da suka yi ba su bayyana wasu muhimman bayanai ba, ba su kuma bayyana ci gaban da aka samu ba, ba a kuma cimma matsaya mai kyau ba, lamarin da ya kara haifar da cece-kuce da rashin fahimta a tsakanin kasashen duniya.

Rasha dai ita ma bangare ne mai muhimmanci a lamarin fashewar bututun iskar gas na Nord Stream. Kasar Sin ta yi kira ga kasashen da abin ya shafa da su himmatu wajen tuntubar juna da hada kai da Rasha tare da gudanar da bincike kan lamarin. Game da wannan batu, yana da muhimmanci a yi watsi da fuska biyu tsakanin kasashen duniya, musamman a cikin kwamitin sulhu, a cewar Geng. (Yahaya)