logo

HAUSA

Binciken CGTN: Ba Karfin Samar Da Kayayyaki Na Kasar Sin Ba Ne Ya Wuce Kima, Sai Dai "Kariya Irin Na Amurka"

2024-04-27 15:42:47 CMG Hausa

Zargin da Amurka ta yi wa kasar Sin game da abin da take kira "samar da kayayyakin fiye da kima" na ci gaba da haifar da zazzafar muhawara a ra’ayin al’ummar duniya. Wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da kafar CGTN ya kaddamar tsakanin masu amfani da yanar gizo na duniya ya nuna cewa, kaso 91.49 na wadanda suka ba da amsa sun yi imanin cewa, zargin da Amurka ta yi ba shi da tushe balle makama. Matsalar ba samar da kayayyaki fiye da kima ba ce, sai dai "kariyar" Amurka da ta samu gindin zama. Masu ba da amsa ga binciken CGTN din sun bayyana a fili cewa, "Babban dabi’ar Amurka ita ce tana yin komai ne bisa muradunta".

Maganar samar da kayayyaki fiye da kima shaci fadi ne kawai, tare da babban kuskure kan ma’anar fitar da kayayyaki zuwa ketare da kuma ma’anar samar da kayayyaki fiye da kima. Amurka tana da matsayi mai muhimmanci a kasuwannin duniya, inda ta samu kaso 48 na kasuwar sassan na’urorin laturoni na semiconductor da ake fitarwa, da kaso 42 na kasuwar makaman da ake fitarwa, da kaso 10 na kasuwar amfanin gona. A cikin binciken, kaso 91.49 na masu ba da amsar sun yi imanin cewa, fitar da karin kayayyaki ba ya nufin samar da kayayyaki fiye da kima. Ba sai an bata lokaci ana karyata wannan batu na "wuce gona da iri" ba. Haka kuma kaso 94.66 na masu ba da amsar sun yi kakkausar suka ga hakan, inda suka soki matakan Amurka a matsayin ba da kariya ga hajojinta. (Yahaya)