logo

HAUSA

Netanyahu ya amince da shirin kaddamar da matakan soji a Rafah

2024-04-26 12:16:44 CMG Hausa

Rahotanni daga kafar watsa labaran gwamnatin Isra’ila, na cewa firaministan kasar Benjamin Netanyahu, ya amince da gudanar da samame ta kasa a birnin Rafah na kudancin zirin Gaza.

Bayan amincewar mista Netanyahu a jiya Alhamis, ana sa ran nan gaba kadan, Isra’ila za ta fara aikin fitar da fararen hula daga Rafah, a shirye shiryenta na fara kaddamar da hare hare. To sai dai kuma rahotannin na cewa Netanyahu bai bayar da umanrnin fara aiwatar da hare haren ba tukuna. (Saminu Alhassan)