Ma`aikatar ma`adinai ta tarayyar Najeriya ta soke lasisin wasu kamfanonin hakar ma`adinai guda 924
2024-04-26 10:48:31 CMG Hausa
Ministan ma`aikatar bunkasa harkokin ma`adinai a tarayyar Najeriya Mr Dele Alake ya sanar da soke lasisin kamfanonin hakar ma`dinai guda 924 wadanda ba a amfani da su ba.
Ministan ya sanar da hakan ne ranar Laraba 24 ga wata a birnin Abuja yayin wani taron manema labarai, ya ce daga cikin lasisin da aka soke sun hada na binciken wuraren da ake da ma`adinai guda 528.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Mr. Dele Alake kuma ya ce sauran kamfanonin da aka soke lasisin nasu sun hada da na hayar wuraren hakar ma`adanai guda 20 da wajen sarrafa duwatsu guda 101 da kuma na kananan kamfanonin hakar ma`adanai gudan 273.
Ministan ya ce ko a cikin watan Nuwanban da ya gabata, ma`aikatar ta soke lasisin izinin ci gaba da aikin hakar ma`adinai ga wasu kamfanoni 1,633 saboda gaza bin ka`idojin aiki.
Ya tabbatar da cewa yanzu haka gwamnati na kokarin tsaftace sha`anin hakar ma`adinai a kasar ta yadda zai yi gogayya da na sauran kasashen duniya, a don haka ne ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da suka tabbatar ba sa bin ka`idojin sana`ar da su sauya hallayarsu.
“Masu lasisi mafi girma, wato lasisin hakar ma`adanai wajibi ne sai su biya gwamantin tarayya tsabar kudi na naira miliyan goma kan kowanne lasisi, kafin a dawo masu da shi, su kuma masu lasisin kananan kamfanonin hakar ma`adanai kuwa za su biya naira miliyan bakwai da dubu dari biyar ne, masu lasisin izinin binciken wuraren ma`adinai kuwa za su biya naira miliyan biyar ne kawai muddin suna bukatar a dawo masu da lasisin da aka soke” (Garba Abdullahi Bagwai)