logo

HAUSA

Sin ta bayyana damuwa game da ci gaban hare haren Isra’ila a Syria

2024-04-26 10:49:20 CMG Hausa

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana matukar damuwar kasarsa, don gane da ci gaban hare haren Isra’ila a yankunan kasar Syria, lamarin da a cewarsa ya yi matukar keta alfarmar ‘yancin kai da yankunan kasar ta Syria. Kaza lika hakan zai kara ta’azzara yanayin yankin, zuwa yanayi da ka iya kaiwa ga gagarar a shawo kan sa.

Geng Shuang, ya ce kakaba takunkumai daga bangare daya, da wawashe albarkatu, sun dade da haifarwa Syria koma baya, a kokarin ta na farfado da tattalin arziki, da bunkasa zamantakewar al’umma, da kyautata rayuwar al’ummun kasa.

Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin na kira ga kasashen da lamarin ya shafa, da su gaggauta aiwatar da haramtattun matakai na kashin kai kan Syria. Har ila yau, ba tare da wani bata lokaci ba kasashen waje su kawo karshen jibge dakaru ba bisa ka’ida ba a kasar.  (Saminu Alhassan)