logo

HAUSA

Ministocin harkokin wajen Argentina, Bolivia da Peru za su ziyarci kasar Sin

2024-04-26 19:15:39 CMG Hausa

 

Bisa gayyatar da mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya yi musu, ministar harkokin waje da cinikayyar duniya da addinai ta kasar Argentina Diana Mondino, za ta kawo ziyara kasar Sin daga ranar 27 ga watan Afrilu zuwa ranar 1 ga watan Mayu, kana ministar harkokin wajen kasar Bolivia Celinda Sosa Lunda da minstan harkokin wajen kasar Peru Javier Gonzalez-Olaechea Franco za su ziyarci kasar Sin daga ranar 28 zuwa 30 ga watan Afrilu, a cewar mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin a yau Juma’a. (Yahaya)