logo

HAUSA

Dalilin Da Ya Sa Duniya Ke Bukatar Karfin Sin Na Samar Da Hajoji Masu Alaka Da Makamashi Mai Tsafta

2024-04-26 16:09:35 CMG Hausa

Kwanan baya, a gun taron makamashi na duniya karo na 26, babban darektan kamfanin Saudi Aramco, daya daga kamfanonin man fetur mafiya girma a duniya Amin H. Nasser, ya bayyana cewa, ana samun ci gaban alluna samar da wutar lantarki ta hasken rana bisa kokarin da Sin take yi na rage farashin su, kuma haka abun yake a fannin motoci masu amfani da makamashi mai tsabta.

A cewar mista Nasser, bunkasuwar sana’o’i masu alaka da makamashi mai tsafta a kasar Sin, ta hanzarta cimma burin kasashen yamma na samun daidaito tsakanin yawan hayaki mai dumama yanayi da za a fitar da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin, kuma Sin ta taka rawar gani wajen karkata ga nau’o’in irin wadannan makamashi da za a iya amfani da su a nan gaba.

A halin yanzu, kasashe daban-daban na yin iyakacin kokarin zamanantar da masana’antun samar da hajoji, da amfani da makamashi mai tsafta, kuma ana matukar bukatar na’urori da sassan injuna dake da alaka da samarwa da amfani da makamashi mai tsabta.

Ban da wannan kuma, kafar yada labarai ta “Bloomberg” ta ba da labari a kwanan baya cewa, “nesa ta zo kusa” a fannin karkata hanyar da duniya ke bi ta amfani da makamashi, saboda yadda Sin take samar da hajoji masu alaka da makamashi mai tsabta masu saukin farashi.

Ya zuwa yanzu, yawan na’urorin samar da wutar lantarki ta amfani da karfin iska, da hasken rana da Sin take samarwa duniya, ya kai kashi 50% da 80%. Daga shekarar 2012 zuwa ta 2021, yawan karuwar ciniki ba tare da gurbata muhalli ba da Sin take gudanarwa ya kai kaso 146.3%, wanda ya karfafa bunkasuwar duniya, da kwarin gwiwa a bangaren samar da makamashi mai tsabta.

Kaza lika, Sin ta taimakawa sauran kasashen wajen daga karfin tinkarar sauyin yanayi ta hanyoyin samar da tallafin fasahohi, da inganta kwarewarsu da tallafin kudade da sauransu.

Wasu ‘yan siyasar Amurka suna fakewa da sunan wai “kasar Sin na samar da hajoji masu alaka da makamashi masu tsabta fiye da kima” wajen aiwatar da manufar kariyar ciniki, matakin da zai illata kokarin da ake yi na karkata hanyar amfani da makamashi a duniya.

Ko shakka babu, matsalar da duniya ke fuskanta ba samar da hajoji masu alaka da makamashi mai tsabta fiye da kima ba ne, domin kuwa ana matukar bukatar irin wadannan hajoji. Kuma Sin tana samar da su ga duniya bisa matsananciyar bukatar da ake da ita. (Amina Xu)