logo

HAUSA

‘Yan sama jannatin kumbon Shenzhou-18 sun shiga tashar binciken samaniya ta kasar Sin

2024-04-26 10:06:01 CMG Hausa

A yau Juma’a ne ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-18, suka shiga tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, inda suka sadu da sauran ‘yan sama jannati uku dake cikin tashar, tare da fara sabon zagayen karbar aiki.

‘Yan sama jannatin kumbon Shenzhou-17, sun bude kofar kumbon su da misalin karfe 5:04 na asubahin Juma’ar nan bisa agogon Beijing, inda suka gaisa da sabbin zuwan, tare da daukar hoto tare da su.

Wannan haduwa tasu, ita ce irinta ta hudu da rukunonin ‘yan sama jannatin kasar Sin suka gudanar, karkashin tsarin karba karbar aiki da ‘yan sama jannatin kasar Sin ke yi a tashar ta binciken samaniya mallakin kasar Sin.

Hukumar lura da binciken sararin samaniyar kasar Sin, ta ce daukacin ‘yan sama jannatin su shida, za su kasance tare, kuma za su yi aiki na kusan kwanaki biyar, domin kammala ayyukan da aka tsara, da kuma mika aiki ga sabuwar tawagar.

Da karfe 9 saura minti 1 na daren jiya Alhamis bisa agogon Beijing ne aka kunna, tare da harba kumbon Shenzhou-18, ta amfani da rokar Long March 2F Yao18, dauke da ‘yan sama jannati uku daga tashar harba kumbuna ta Jiuquan. (Saminu Alhassan)