Sin: Bai Kamata Turai Ya Bukaci Sin Da Ta Tinkarar Matsalar Sauyin Yanayi Yayin Da Take Dakile Masana’antar Sabbin Makamashin Sin Ba
2024-04-26 20:15:00 CMG Hausa
An gudanar da taron tattaunawa game da yanayi na Petersburg a kwanan baya a birnin Berlin na kasar Jamus.
Yayin da ya amsa tambayar da aka yi masa yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya ce, kasar Sin ta yi la’akari da kyawawan kalamai na ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock. A sa’i daya kuma, Wang Wenbin ya jaddada cewa, a baya-bayan nan kungiyar tarayyar Turai ta EU ta dauki wasu matakan kasuwanci kamar kaddamar da bincike kan motocin Sin masu aiki da sabbin makamashi, da na’urorin samar da wutar lantarki bisa karfin iska, lamarin da ke nuni da alamar ba da kariyar ciniki. Bai kamata kungiyar ta EU ta bukaci kasar Sin ta ba da gudummawarta wajen tinkarar sauyin yanayi, yayin da take takaita karfin masana’antar sabbin makamashi na kasar Sin ba. Irin wannan tsari mai cin karo da juna ba kawai zai cutar da ita kanta EU kadai ba, har ma zai gurgunta kokarin da duniya ke yi na tinkarar sauyin yanayi. (Yahaya)