Wang Yi ya yi shawarwari da Antony Blinken a Beijing
2024-04-26 10:40:05 CMG Hausa
Yau Jumma’a, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Amurka Antony Blinken a birnin Beijing, a ci gaba da ziyarar aiki da mista Blinken din ke yi a nan kasar Sin.
Yayin zantawarsu, Wang Yi ya yi tsokaci kan huldar kasashen biyu. A cewarsa, huldar kasashen biyu tana dan kara kyautata karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, amma a wani bangare na daban, wasu abubuwan dake kawo cikas ga huldarsu na kara karuwa.
Wang, ya kuma jadadda cewa, Sin na tsayawa kan raya huldar kasashen biyu bisa ra’ayin kafa kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya, kuma tana tsayawa tsayin daka kan ka’idar da Xi Jinping ya gabatar, wato mutunta juna, da zama tare cikin lumana, da hadin kai, da cin moriya tare.
Kaza lika, Sin na fatan bangarorin biyu za su mai da hankali kan muradun da suka fi jawo hankalinsu, da fatan Amurka za ta kaucewa tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, da yiwa bunkasuwar Sin matsin lamba. Kana ta kauracewa keta tushen muradun Sin, wato bangaren ikon mulkin kasar, da tsaro da bunkasuwa. (Amina Xu)