logo

HAUSA

Mutane 13 sun rasu sakamakon hadarin mota a tsakiyar kasar Senegal

2024-04-26 11:06:07 CMG Hausa

Rahotanni daga kamfanin dillancin labarai na kasar Senegal, na cewa wani hadarin mota a yankin tsakiyar kasar ya yi sanadin rasuwar mutane 13, tare da jikkatar wasu mutanen 40.

Kamfanin dillancin labaran kasar ya hakaito wata majiyar jami’an tsaro na cewa, hadarin ya auku ne da misalin karfe 7 na daren jiya Alhamis, a kan babbar hanya mai lamba 1, kusa da kauyen Yamong na yankin Kaffrine dake kasar.

Majiyar kafar watsa labaran, ta ce hadarin ya faru ne sakamakon fashewar da tayar wata bas mai dauke da fasinjoji ta yi, wanda hakan ya sanya bas din kifewa, tare da hallaka mutane 13 da jikkata wasu da dama. (Saminu Alhassan)