logo

HAUSA

Sakamakon binciken CGTN ya karkata ga goyon bayan tsagaita wuta da kawo karshen yaki tsakanin Falasdinu da Isra’ila

2024-04-26 16:43:55 CMG Hausa

Wani binciken jin ra’ayin jama’a da kafar watsa labarai ta CGTN ta kasar Sin ta gudanar ya nuna cewa, kaso 90.05 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu, sun yi kira da babbar murya ga bangarorin Isra’ila da Falasdinu da su dakatar da bude wuta nan take, domin kaucewa kara tabarbarewar yanayin jin kai.

Kaso 93 bisa dari na masu bayyana ra’ayin kuwa, na ganin tabbas ya dace kwamitin tsaron MDD, ya aiwatar da matakin shiga tsakani da nufin kaucewa kara kazantar tashin hankalin.

Kaza lika, kaso 92 bisa dari ya amince da bukatar kasashen waje, ta su dakatar da aikewa da makamai, da sauran na’urorin aikin soji ga bangarorin biyu, kana a gaggauta aiwatar da duk wasu matakai daka iya ta’azzara yanayin da ake ciki.

Bugu da kari, kaso 88 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu, sun yi matukar goyon bayan hada karfi da karfe tsakanin sassan kasa da kasa wajen cimma adalci, da wanzar da cikakkiyar nasarar shawo kan matsalar Falasdinu. Har ila yau, sun jaddada cewa, duk yawan yarjejeniyoyi da za a cimma game da batun Gaza, dole ne su kasance masu martaba buri, da zabin kashin kai na al’ummar Falasdinu, ba wai wadanda za a kakaba musu ba.

An gudanar da kuri’un jin ra’ayin jama’ar ne kan dandalolin kafar CGTN na Turanci, da Sifaniyanci, da Faransanci, da Larabci, da harshen Rasha, inda masu bayyana ra’ayoyi sama da 11,000 suka kada kuri’un su cikin sa’o’i 24. (Saminu Alhassan)