logo

HAUSA

Yawan Kayayyakin Da Sin Ta Samar Ya Wuce Misali Ko Damuwar Amurka Ta Wuce Kima?

2024-04-26 08:47:32 CMG Hausa

Ran 24 ga wata, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya fara ziyarar aiki a kasar Sin, karo na biyu a wa’adin aikinsa. Bisa labarin da kafofin yada labarai na Amurka suka bayar, an ce, Blinken zai ci gaba da shafawa kasar Sin bakin fenti kamar yadda sakatariyar baitul malin kasar Janet L. Yellen ta yi, kan wasu bangarorin da Sin take da fifiko sama da Amurka, da cewa wai “Yawan kayayyakin da masana’antun Sin ke samarwa ya wuce kima”. Amma ko da gaske ne yawan kayayyakin da Sin ta samar ya wuce misali, ko yawan damuwar Amurka ya wuce kima?

Bari mu duba wasu alkaluma. Hukumar kula da makamashi ta duniya wato IEA ta yi kiyasin cewa, domin cimma burin samun daidaito tsakanin yawan hayaki mai dumama yanayi da za a fitar da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin, zuwa shekara ta 2030, za a bukaci motoci masu amfani da makamashi mai tsabta kimanin miliyan 45, yayin da za a bukaci wutar lantarkin da yawansa ya kai gigawatt 820 daga sabbin injunan samar da wutar lantarki masu amfani da hasken rana. Wadannan alkaluma sun ninka sau 4.5 da 4 bisa na shekarar 2022. A matsayin kasa mafi karfi a fannin samarwa da sayar da motoci masu amfani da makamashi mai tsabta, kasar Sin ta samar da motocin da yawansu ya kai fiye da miliyan 9.5 a bara, kuma ta fitar da kimanin miliyan 1.2 ketare. Wato adadin da ya kai kusan kashi 90% na biyan bukatun cikin gidan kasar ta Sin. Abin da ya bayyana cewa, karancin samar da hajoji masu alaka da makamashi mai tsabta matsala ce da duniya ke fuskanta, a maimakon a ce an samar da su fiye da kima. Kasashen duniya na matukar bukatar nagartaccen karfin samar da hajojin da Sin take da shi.

Damuwa da rashin kwarin gwiwa da Amurka ke da su na tilasta mata daukar matakan shafawa kasar Sin bakin fenti kan sana’o’inta da ke da fifiko, don mai da su barazanar da za ta sanya sauran kasashe fargaba. Amma, ba za a iya mai da baki fari ba, mataki daya tilo da Amurka za ta dauka wajen rage damuwarta ita ce, ta kara karfin kirkire-kirkire da hadin kai don more ci gaba tare. Kamata ya yi Amurka ta mai da hankali kan kyautata kwarewarta, a maimakon gurbata gaskiya da shafawa wasu bakin fenti, tana cewa wai hajoji masu nasaba da makamashi mai tsabta da Sin ta samar na dogaro da rangwamen da gwamnatin Sin ke bayarwa, wanda ya illata kasuwarta. To, kara karfin takara ba shi da alaka da magana ko furucin da aka yi, ya dogara ne da nagartaccen matakin da za a dauka. (Mai zana da rubuta: MINA)