logo

HAUSA

Sama da fursunoni 100 sun tsere daga wani gidan yari a Nijeria

2024-04-25 20:30:32 CMG Hausa

 

Akalla fursunoni 119 ne suka tsere a daren ranar Laraba, daga gidan yarin Suleja na jihar Neja dake arewa maso tsakiyar Nijeriya, wanda ruwan sama ya lalata.

Kakakin hukumar kula da gidajen yari na kasar Samson Duza, ya bayyana cikin wata sanarwa a jiya cewa, an kama 10 daga cikin fursunonin da suka tsere tare da sake kulle su.

A shekarun baya-bayan nan, Nijeriya ta fuskanci jerin masu tserewa daga gidajen yari, lamarin da ya sa gwamnatin kasar ta kaddamar da bincike a gidajen yarin dake fadin kasar, domin magance matsalolin dake haifar da tserewar. (Fa’iza Mustapha)