logo

HAUSA

Sin ta ba da tallafin abinci ga yara 165,000 a Karamoja na Uganda

2024-04-25 12:59:34 CMG Hausa

Kasar Sin ta ware kudade ta hannun hukumar samar da abinci ta MDD wato WFP domin samar da abinci a makarantu ga yara sama da 165,000 daga makarantu 315 a Karamoja dake arewa maso gabashin Uganda.

Gudunmawar wani bangare ne na kudirin kasar Sin na inganta wadatar abinci da abinci mai gina jiki, da karfafa rayuwar jama'a, da bunkasa tattalin arziki a yankin, a cewar Zhang Lizhong, jakadan kasar Sin a Uganda, yayin da yake jawabi a bikin mika kayayyakin a jiya Laraba.

A cewar WFP, tallafin zai ba damar sayo masara da wake da kuma man girki ga yaran Karamoja. (Yahaya)