logo

HAUSA

Ma’Aikatar Kasuwancin Sin Ta Maida Martani Kan Binciken Ba-Zata Da Eu Ta Gudanar Kan Kamfanonin Sin Dake Turai

2024-04-25 14:11:42 CMG Hausa

Jiya Laraba a gun wani taron manema labarai, jami’in hukumar lura da manufofin cinikayyar sassan waje dake karkashin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya amsa tambayoyin da aka yi masa game da binciken ba-zata da EU ta yiwa ofisoshin kamfanonin Sin dake Turai, inda ya bukaci bangaren Turai da ya dakatar da matakin kuskure nan da nan, da samar da yanayin zuba jari mai bude kofa da adalci da daidaito ba tare da nuna bambancin ra’ayi ga kamfanonin kasa da kasa ba.

A cewarsa, EU ba ta aike da sako da wuri ba kuma ba ta ba da sanarwa ba, har ta kutsa kai cikin ofisoshin kamfanonin Sin ba zato ba tsamani, da dakatar da na’urori da injunan aikinsu, abin da ya sabawa ka’idoji, kuma ya kawo cikas ga yanayin takarar kasuwa cikin adalci da daidaito, kazalika ya illata kwarin gwiwar kamfanonin waje dake Turai, hakan ya bayyana cewa, yanayin kasuwancin Turai na kara tabarbarewa. Sin na matukar rashin jin dadi kan hakan, kuma za ta ci gaba da mai da hankali kan matakan da Turai za ta dauka, tare da daukar matakai da suka wajaba, don kare halastattun muradun kamfanoninta. (Amina Xu)