logo

HAUSA

Yadda za mu fahimci kuskuren Amurka na cewa wai kasar Sin “ta wuce gona da iri” wajen samar da hajoji

2024-04-25 13:44:16 CMG Hausa

Kwanan baya, Amurka ta zargi kasar Sin, cewa wai yawan hajoji masu amfani da makamashi mai tsabta da Sin ta samar ya wuce kima, kuma ta mai da batun a matsayin sabon makamin kaiwa tattalin arzikin Sin hari. Bari mu tantance wannan maganar.

Da farko, wasu mutanen Amurka sun alakanta yawan hajojin da ake samarwa da cinikin kasa da kasa, inda suke ganin cewa, kara fitar da hajoji zuwa kasashen waje na nufin yawan hajojin da aka samar ya wuce gona da iri. Amma, irin wannan tunanin ya saba da manufar tattalin arziki, kana ya saba da dunkulewar duk duniya baki daya.

Sai dai kuma wasu mutanen Amurka sun canza maganar cewa, wai yawan kayayyaki masu amfani da makamashi mai tsabta da Sin ta samar ya wuce bukatun duniya. Ko gaskiya ne wannan? Bari mu duba wasu alkaluma, inda hukumar kula da makamashin duniya wato IEA ta yi kiyasin cewa, domin cimma burin samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za a fitar da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin, zuwa shekara ta 2030, za a bukaci motoci masu amfani da makamashi mai tsabta kimanin miliyan 45, yayin da za a bukaci wutar lantarkin da yawansa ya kai gigawatt 820 daga sabbin injunan samar da wutar lantarki masu amfani da hasken rana. Wadannan alkaluma sun ninka sau 4.5 da 4 bisa na shekarar 2022.

Alkaluman na bayyana cewa, kawo yanzu yawan hajojin da Sin ta samar bai biya bukatun kasuwa ba, musamman ganin yadda kasashe masu tasowa ke da bukata mai tarin yawa kan kayayyaki masu amfani da makamashi mai tsabta. A matsayin kasa mafi girma dake da babbar kasuwar samar da makamashin da ake iya sake amfani da shi, wadda kuma ke kera na’urori da injuna a wannan fanni, ana matukar bukatar ingantattun kayayyakin da kasar Sin za ta samar. (Amina Xu)