logo

HAUSA

An kaddamar da gagarumin shirin inganta tsarin samar da abinci mai gina jiki a tarayyar Najeriya

2024-04-25 09:39:14 CMG Hausa

Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya yi kira ga sarakunan kasar da kuma shugabannin addinai da su bayar da hadin kan da ya kamata a shirin gwamnati na samar da ingantaccen abinci mai gina jiki ga al`ummomin kasar baki daya.

Ya yi wannan kiran ne ranar 23 ga wata a babban dakin taro dake fadar shugaban kasa dake birnin Abuja, yayin wani taro da shugabannin al`umma dake kasar wanda aka yi wa taken  “rawar da sarakuna da shugabannin addinai za su taka wajen tabbatar da kwazon dan adam ta hanyar wadatuwar abinci mai gina jiki”

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Mataimakin shugaban kasar ya ce burin gwamnatin Najeriya bai tsaya kawai ga samar da wadataccen abinci ba, ya hada da  da samar da ingantattun nau`ikan abinci masu sinadaran gina jiki.

Sanata Kashim Shettima ya ce ya zama wajibi mu sanar da duniya cewa da gaske muke wajen fafutukar yakar illolin dake tattare da karancin abinci mai gina jiki ga rayuwar dan adam, a don haka ne ma, ya yi kira da babbar murya ga shugabannin addinai da sarakunan kasar da suka halarci taron da su marawa wannan kokarin na gwamnati bisa la` akari da tasirin da suke da shi wajen tabbatar da hadin kai da fahimtar juna a kasar.

“Shugaban kasa ya amince a ware kaso 20 na tallafin kayan abinci ga kungiyoyin addinai da kuma masarautu, za a bayar da kulawa ta musamman kuma a wannan tallafi ga makarantun tsangaya da kuma na mushan, za kuma a rabar da kayan abincin ne ta hannu ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki  na kasa”

A don haka mataimakin shugaban kasar ya bukaci sarakuna da shugabannin al`umma kana da shugabannin addinai da su himmatu wajen nunawa mabiyansu a wuraren ibada ko kuma a wuraren tarukan al`adu alfanun  abinci mai gina jiki.(Garba Abdullahi Bagwai)