logo

HAUSA

Tallafin Shirye-shiryen Yaki Da Cutar Malaria Da Sin Ta Bayar Ya Haifar Da Kyakkyawan Fata Ga Al’ummar Afrika

2024-04-25 20:25:00 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa kasar Sin ta samar da tallafi mai yawa na yaki da cutar cizon sauro ta Malaria ga kasa da kasa, ta hanyar amfani da maganin Artemisinin wajen samar da magunguna da tallafin kwararru da ginin cibiyoyin yaki da cutar da horar da jami’ai.

Ya ce, a nahiyar Afrika, shirye-shiryen yaki da cutar da magunguna da dabarun kasar Sin, sun samar da fatan rayuwa ga mutanen nahiyar da dake fama da cutar.

Ya kara da cewa, kasar Sin na dogaro da cibiyar bincike da horo kan kawar da cutar Malaria ta MDD, wajen horar da sama da jami’an lafiya da masana 2,000 daga kasashe da yankuna 85, game da kandagarki da takaita cutar Malaria da sauran cututtuka masu yaduwa.

A cewar hukumar lafiya ta duniya (WHO), kimanin mutane miliyan 240 a yankin kudu da hamadar Sahara kadai, sun amfana da hadin maganin Artemisinin. (Fa’iza Mustapha)