Sin ta yi kira da a ba da taimako ga yankin manyan tabkunan Afirka
2024-04-25 09:54:14 CMG Hausa
Wakilin kasar Sin ya yi kira ga kasashen duniya da su taimaka wajen inganta zaman lafiya da tsaro da ci gaba a yankin manyan tabkunan Afirka a jiya Laraba.
Duk da kokarin da kasashen yankin ke yi, yanayin tsaro mai rauni, da tashe-tashen hankula, da kuma mummunan halin jin kai a yankin manyan tabkuna sun kasance abin matukar damuwa. Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Fu Cong ya bayyana cewa, ya kamata kwamitin sulhu na MDD da kasashen duniya baki daya su kara mai da hankali da zuba jari ga yankin da kuma ba da karin tallafi.
Da farko dai, dole ne a dakatar da tashin hankali nan take da kuma sassauta al'amura, kamar yadda ya shaida wa taron kwamitin sulhu kan yankin manyan tabkuna.
Na biyu, ya kamata kasashen duniya su goyi bayan kokarin yankin na tabbatar da tsaron bai daya.
Na uku, yana da muhimmanci a inganta ci gaba tare da gina ginshikin zaman lafiya.
Talauci da rashin ci gaba su ne ummul aba'isin tashe-tashen hankula da suka dade suna addabar yankin manyan tabkuna. Ya kamata kasashen duniya su taimaka wa kasashen yankin wajen tunkarar kalubalen ci gaban da ake fuskanta, da kara kaimi ga ayyukan jin kai, da kara karfin kasa na samun bunkasuwa, da nufin samar da zaman lafiya ta hanyar ci gaba. (Yahaya)