logo

HAUSA

Aljeriya da Tunisiya da Libya sun amince da sarrafa ruwan karkashin kasa a Sahara

2024-04-25 10:25:57 CMG Hausa

Kamfanin dillancin labaran APS ya bayar da rahoto a jiya Laraba cewa, kasashen Aljeriya, Tunisiya da Libya, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya a birnin Algiers domin kafa tsarin tuntubar juna kan yadda za su tafiyar da albarkatun ruwan karkashin kasa a yankin Sahara.

Ministan makamashi na kasar Aljeriya Taha Derbal, da ministan noma, albarkatun ruwa, da kamun kifi na Tunisiya Abdelmonem Belati, da mataimakin ministan albarkatun ruwa na Libya Mohammed Faraj Qunidi, suka rattaba hannu kan yarjejeniyar, inda suka jaddada muhimmancin zurfafa fahimtar juna da karfafa musayar bayanai game da albarkatun ruwa na bai daya na kasashen.

Aljeriya, Tunusiya da Libya suna da babban magudanar ruwa na karkashin kasa a kan iyakar hamadar da ta hada kasashen, wadda ake daukar ta a matsayin daya daga cikin manyan wuraren ruwan karkashin kasa a duniya, inda kashi 70 cikin 100 na yawan ruwan ke cikin kasar Aljeriya. (Yahaya)