logo

HAUSA

Sin: Ba Za A Taba Amincewa Da Kawo Tsaiko Ga Yunkurin Kwamitin Sulhun MDD Na Ingiza Tsagaita Bude Wuta A Gaza Ba

2024-04-25 20:15:10 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce ci gaba da yaki a Gaza, abu ne da ba za a lamunta ba, kuma kisan gillar da ake wa yara da mata, abu ne da ba za a yi hakuri da shi ba, haka kuma ba za a taba amincewa da kawo tsaiko ga yunkurin Kwamitin Sulhu na MDD na ingiza tsagaita bude wuta ba.

Wang Wenbin ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau Alhamis, inda ya ce kasar Sin na bukatar kasashe masu ruwa da tsaki, su daina kawo tsaiko kan matakan Kwamitin Sulhun, tare da kira ga bangarorin da batun ya shafa su aiwatar da kudurin Kwamitin Sulhun mai lamba 2728, da cimma tsagaita bude wuta mai dorewa nan take kuma ba tare da gindaya sharadi ba. Bugu da kari a tabbatar da samar da agajin jin kai mai dorewa ba tare da katsewa ba, domin kawo karshen wahalhalun da al’ummar Palasdinu ke fuskanta da daina kunyata wayewar kan bil Adama. (Fa’iza Mustapha)