logo

HAUSA

Ko ziyarar Antony Blinken a kasar Sin za ta banbanta da ta sauran jami’an Amurka?

2024-04-25 15:26:00 CMG Hausa

Da yawa daga masu fashin baki na hasashen cewa, mawuyaci ne a samu wani babban sauyi a ziyarar da sakataren wajen Amurka Antony Blinken zai gudanar a kasar Sin, tsakanin ranar Laraba zuwa Jumma’a, musamman duba da cewa an shiga shekarar babban zaben shugabancin Amurka, irin lokacin da abun da kadai ke hade kan manyan jam’iyyun kasar wato Democrat da Republican, shi ne sukar kasar Sin domin jan ra’ayin Amurkawa da samun kuri’u, amma duk da haka, yana da kyau, ganin babban jami’in na Amurka zai gudanar da ziyara a kasar Sin a irin wannan lokaci.

Haka dai abun yake, idan mun waiwayi ziyarar da sakatariyar cinikayyar Amurka Gina Raimondo ta gudanar a kasar Sin a shekarar bara, da wadda sakatariyar baitul-malin Amurka Janet Yellen ta gudanar a farkon watan nan na Afirilu, da ma dawo da tattaunawa ta kafar bidiyo tsakanin ministocin tsaro na kasashen biyu, wato Lloyd Austin, da takwaran aikinsa na Sin Dong Jun a farkon watan nan.

Ko shakka babu, Bahaushe kan ce “Yawan gaisuwa ya fi yawan fada”, wato dai yawan tattaunawa tsakanin sassan biyu, ya fi a ce ana zaman doya da man ja, to amma kuma yawaitar matakan takunkumi kan kamfanonin Sin, da shafawa Sin din kashin kaji da Amurka ke yi, yana bayyana akasin kalaman neman hadin kai da jami’an Amurkan ke furtawa.

Akwai tarin ayyuka da ya dace a gudanar, domin kyautata dangantakar Sin da Amurka, da kuma matakai na kaucewa ci gaba da tabarbarewar alakar tattalin arziki da siyasa tsakanin sassan biyu.

Da farko dai, wajibi ne a yi watsi da batun "Raba Gari". Kuma hakan zai tabbata ne kawai idan har Amurka ta yi fatali da kokarin danne kamfanonin Sin, irin su babban kamfanin fasahohin sadarwa na Huawei, da fakewa da batun “Tsaron Kasa”, don baiwa kasuwar Amurka kariyar cinikayya, da shawo kan batun haramtawa kamfanonin kirar sassan laturoni na “Chips” na Amurka sayar da hajojin su ga kasuwannin Sin da dai saura su.

Maimakon daukar matakan zargi, da danniya, da kariyar cinikayya da nuna son kai, kamata ya yi Amurka ta hada gwiwa da kasar Sin, da ma sauran kasashen duniya, wajen gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil Adama, ta yadda moriyar bai daya ta dukkanin sassa za ta zarce ta kashin kai. A daya bangaren kuma, nuna fuska biyu, da fada ba cikawa, ba abun da za su haifar illa raba kawuna, da gurgunta amincewa da juna, da lalata moriyar duniya baki daya.( Saminu Alhassan)