logo

HAUSA

An gudanar da taron tattauna makomar kasa a tarayyar Najeriya inda mahalarta suka nuna bukatar samar da `yan sandan jahohi

2024-04-24 10:16:06 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin kyautata sha`anin tsaron cikin gida tare kuma da sake fasalin ayyukan rundunar `yan sandan kasar.

Ya tabbatar da hakan ne a farkon wannan mako a birnin Abuja yayin taron yini daya a kan makomar kasa, taron mai taken muhawara kan bukatar samar da `yan sandan jahohi ya samu halartar sarakuna da `yan siyasa da tsoffin shugabannin kasar da sauran masu ruwa da tsaki kan sha`anin tsaro.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaban na tarayyar Najeriya wanda ya samu wakilcin mataimakin sa Sanata Kashim Shettima ya ce wajibi ne a yi maganin fargabar da ake da ita, a game da samar da `yan sandan jahohi kafin zartar da wani abu.

 “Abin lura a nan shi ne ra` ayi kan shawarar samar da `yan sandan jahohi ba al`amari ne da ya shafi siyasa, mahimmin batu ne da yake da alaka da garambawul ga dokokin da suke da nasaba da tabbatar da doka da oda a kasa.”

Shi kuwa tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan cewa ya yi yana goyon bayan samar da `yan sandan jahohi  amma kuma:

“Ba ina nufin jahohin su mallaki rokokin ba ne, sai dai akwai bukatar su mallaki manyan makaman zamani bisa la`akari da irin nau`ikan makaman da `yan ta’adda ke amfani da su.”

A gudumowar daya bayar yayin taron, tsohon shugaban kasa Janaral Abdulsalami Abubakar shawara ya bayar kafin a kai ga samar da `yan sandan jahohin.

“Idan har magana muke yi na kirkirar `yan sandan jahohi, yana da kyau mu yi la`akari kuma da rawar da sarakuna za su taka.”

A karshe a nasa jawabin, sefeton janaral na `yan sandan Najeriya Mr Kayode Agbetokun, ya ce Najeriya ba ta kai matsayin samar da `yan sandan Jahohi ba a yanzu.

“Samar da `yan sandan jahohi a halin yanzu zai kara ruruta rikicin kabilanci a kasa, kuma za a rinka samun umarni biyu a lokaci guda a jahohi.” (Garba Abdullahi Bagwai)