logo

HAUSA

Kenya na kara rungumar fasahohin sufuri marasa gurbata muhalli irin na kasar Sin

2024-04-24 12:05:38 CMG Hausa

Babban sakatare a ma’aikatar makamashi da albarkatun man fetur ta kasar Kenya Alex Wachira, ya jinjinawa fasahohin amfani da ababen hawa masu aiki da lantarki na kasar Sin, a gabar da Kenya ke kara rungumar wadannan fasahohi na sufuri marasa gurbata muhalli.

Wachira, ya yi tsokacin ne yayin taro karo na biyu, na masu ruwa da tsaki a fannin amfani da ababen hawa masu aiki da lantarki na Kenya, inda ya ce ababen hawa masu aiki da lantarki kirar kasar Sin ko EVs, suna maye gurbin ababen hawa masu kona man fetur da aka saba amfani da su. Jami’in ya kara da cewa, "Ina taya daukacin kamfanonin kasar Sin masu sarrafa hajojin wannan fanni a cikin gida murna, bisa rawar gani da suke takawa, wajen ingiza ci gaban kasuwar ababen hawa masu amfani da lantarki a Kenya".

Taron na yini biyu da ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya, ya hallara sama da wakilai 200, ciki har da jami’an gwamnati, da masu ba da tallafi, da kwararru a fannin masana’antun kera ababen hawa masu aiki da lantarki daga sassan kasa da kasa, wadanda suka mayar da hankali ga nazartar hanyoyin kere-kere, da lalubo dabarun rage, ko kawo karshen fitar da iskar carbon mai dumama yanayi a fannin sufuri. (Saminu Alhassan)