logo

HAUSA

Xi ya aike da wasikar taya murna ga dandalin farko na tattauna hadin gwiwa a harkokin sama jannati na Sin da CELAC

2024-04-24 14:11:16 CMG Hausa

A yau Laraba ne aka kaddamar da dandalin farko na tattauna hadin gwiwar harkokin sama jannati, tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka da Karebiya a birnin Wuhan na lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin.

Yayin bikin bude dandalin, mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Guoqing, ya karanta wasikar shugaba Xi Jinping, ta taya murnar bude taron.

Cikin wasikar, shugaba Xi ya ce a bana ake bikin cika shekaru 10, tun bayan da shugabannin sassan biyu suka ayyana kafuwar dandalin. Ya ce Sin da kasashen Latin Amurka da Karebiya, sun cimma manyan nasarori a tsawon sama da shekaru 10 da suka gabata, a fannonin hadin gwiwa daban daban, karkashin dandalin na China-CELAC, wanda hakan ya ingiza shiga sabon zamani na daidaito, da cimma moriyar juna, da kirkire kirkire, da gudanar da harkoki a bude, da sada al’ummun su da alherai na zahiri.

Kaza lika, shugaba Xi ya ce a shekarun baya bayan nan, Sin da kasashen Latin Amurka da Karebiya, sun cimma sakamako masu gamsarwa a fannin ayyukan sama jannati, ciki har da fannin aiki da taurarin dan adam masu tattara bayanan doron kasa, da na sadarwa, da tsarin ayyukan tashoshin sararin samaniya masu nisa, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen ingiza ci gaban kimiyya da fasahohi, da karfafa hade yankunan duniya daban daban, da kyautata rayuwar al’ummun su. (Saminu Alhassan)