logo

HAUSA

Yadda Amurka ke yayata jita-jita game da motocin dake aiki da lantarki na Sin

2024-04-24 15:43:24 CMG Hausa

 

Kwanan baya, gwamnatin Amurka ta sanar da kaddamar da bincike kan motoci masu amfani da wutar lantarki da Sin ta kera bisa hujjar tsaron kasar. Shin ko wadannan motoci za su iya kawo barazana ga tsaron Amurka? Bincike da Amurka ke gudanarwa na kan gaskiya?

Pony AI, wani kamfanin kasar Sin ne dake samar da hidima dangane da motoci marasa matuka. A watan Yuli na bara, ‘yan majalisar dokokin Amurka 4, sun rubutawa ministan kasuwancin kasar Gina Raimondo, da ministan sufurin kasar Pete Buttigieg wasika, wadda a cikinta suka ce kamfanin ya yi rajista, da gudanar da aikin gwaji a California, jihar mafi yawan jama’a a Amurka, da burin tattara bayanan karin al’ummar Amurka. Wadannan ‘yan majalisa sun mai da kamfanin Pony AI, a matsayin misali a cikin korafin da suka gabatar.

To ko mene ne gaskiyar lamarin? Labarin da aka bayar na nuna cewa, tun daga watan Mayu na shekarar 2022, an hana kamfanin gudanar da aikinsa a kasuwar Amurka. Zargin da aka yi game da satar bayanan da kamfanin ya yi ba su da tushe ko kadan. Kaza lika sau da dama an gano irin wannan yanayi, kuma burinsu shi ne hana kamfanonin kasar Sin masu karfin kirkire-kirkire, shiga kasuwannin Amurka bisa hujjar tsaron kasar.(Amina Xu)