logo

HAUSA

An bukaci masana’antun kasashen Afirka da su kyautata amfani da mazuban kayayyakin da suke sarrafawa domin cin gajiyar AfCFTA

2024-04-24 10:44:55 CMG Hausa

Shugaban ofishin kungiyar mamallaka kamfanonin kasar Ghana Seth Twum-Akwaboah, ya yi kira ga sassan masu ruwa da tsaki a harkokin masana’antun sarrafa hajoji na kasashen Afirka, da su mayar da hankali ga kyautata irin mazuban da suke amfani da su domin jan ra’ayin masu sayayya, matakin da a cewarsa ke da matukar muhimmanci, ga cimma gajiya daga damammakin dake akwai a yarjejeniyar cinikayya cikin ‘yanci ta Afirka ko (AfCFTA).

Seth Twum-Akwaboah, ya yi kiran ne a jiya Talata, yayin wata zantawa da manema labarai, a gefen taron nune nune masu nasaba da sarrafa hajoji, da amfani da mazubai na Ghana, ko “Propak Ghana”. Ya ce yarjejeniyar AfCFTA ta samar da babbar kasuwa da nahiyar Afirka za ta ci gajiyarta. To sai dai kuma, akwai kalubalen na yiwuwar a yi awon gaba da wannan dama, muddin kamfanoni da masana’antun nahiyar suka gaza yin gogayya yadda ya kamata, da takwarorin su na sauran sassan duniya.

Mista Twum-Akwaboah ya kara da cewa, hajojin da ake sarrafawa a Ghana suna da matukar inganci, wanda ka iya jure duk wata takara daga waje, amma dole sai an samarwa hajojin mazubai masu jan hankali, idan ana fatan su yi gogayya da na sauran kasashen duniya.

Ya ce “Dole ne kowa ya kawata hajojin sa ta yadda za su samu karbuwa sosai a kasuwanni, duba da cewa masu sayayya na farawa ne da duba yanayin kaya a hannun su, su duba mazubi, da kuma yanayin abun da ke ciki. A daidai wannan gaba, mai sayayya na yanke shawara ne bisa mazubin kayan".  (Saminu Alhassan)