logo

HAUSA

Hatsin da kasar Sin ke samarwa a lokacin zafi na da makoma mai haske

2024-04-24 00:00:40 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da harkokin gona da yankunan karkarar kasar Sin ko kuma MARA a takaice, ta bayyana cewa, yawan hatsi gami da sauran wasu nau’o’in amfanin gona masu samar da mai da kasar Sin ke samarwa a lokacin zafin bana, na bunkasa yadda ya kamata wanda ke da makoma mai haske, kuma yawan alkamar lokacin sanyi da tsirran Rapeseed da ake samarwa a bana, ya zarce na makamancin lokacin bara.