logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Bayyana Zargin Ministocin Harkokin Wajen Kasashen G7 A Matsayin Mara Kan Gado

2024-04-24 20:23:44 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta mayar da martani ga sanarwar ministocin harkokin wajen kasashen G7 dake zargin kasar da wuce gona da iri wajen samar da kayayyaki, inda ta ce, irin wannan zance da ake yayatawa ba shi da tushe, kuma Sin na adawa da shi.

A baya-bayan nan ne ministocin harkokin wajen kasashen G7 suka fitar da wata sanarwar hadin gwiwa, wadda ta ruwaito su suna cewa, manufofi da matakan kasar Sin da ba na kasuwa ba, sun haifar da wuce gona da iri wajen samar da kayayyaki.

Da yake bayani a yau Laraba, yayin taron manema labarai na kulla-yaumin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ba da misali da masana’antar makamashi mai tsafta, domin bayyana karfin kasar Sin a bangaren a matsayin mai inganci, kuma wanda ake bukata wajen ingiza ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, maimakon kiran shi da wuce gona da iri.

Ya ce, babbar matsalar da duniya ke fuskanta yanzu ba karfin samar da kayayyaki fiye da kima a bangaren sabon makamashi ba ne, sai dai matukar karancin hakan. A cewarsa, raya fasahohi da kayayyaki marasa gurbata muhalli da Sin ke yi, musammam masana’antar sabon makamashi, na biyan bukatun dukkan kasashe wajen rage matsalolin makamashi da shawo kan sauyin yanayi. Haka kuma, zai bayar da gudunmuwa ga yunkurin duniya na komawa ga amfani da makamashi mai tsafta da rage hayakin Carbon.

Wang Wenbin ya jaddada cewa, ikirarin da ake cewa Sin na wuce gona da iri wajen samar da kayayyaki, dalili ne kawai na daukar matakan kariyar cinikayya. Ya ce, hana kasar Sin fitar da kayayyaki masu amfani da sabon makamashi kamar motoci masu aiki da lantarki, yanayi na asara kawai zai haifar. (Fa’iza Mustapha)