logo

HAUSA

Moussa Faki Mahamat ya bayyana damuwa game da kara tabarbarewar barazanar tsaro a wasu sassan Afirka

2024-04-24 11:26:52 CMG Hausa

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar AU Moussa Faki Mahamat, ya bayyana matukar damuwa bisa karuwar kalubalen ta’addanci, da tashe tashen hankula na kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi, wadanda ke yin mummunan tasiri a sassan nahiyar Afirka.

Wata sanarwa da ofishin AUn ya fitar a ranar Litinin a birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya, ta hakaito mista Mahamat na cewa, "Ta’addanci da tashe tashen hankula da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi ke haifarwa, su ne manyan laifuka mafiya cutarwa a wannan lokaci, wadanda kuma tuni suka yadu zuwa dukkanin yankuna biyar na nahiyar Afirka". Sanarwar ta ce Mahamat ya bayyana hakan ne ga mahalarta taron manyan jami’ai game da yaki da ta’addanci da ya gudana a ranar Litinin a birnin Abuja.

Faki ya kwatanta matsalar ta’addanci dake addabar nahiyar Afirka da wani “Mummunan ciwon daji mai kisa”, lokacin da yake tsokaci kan halin da ake ciki a yankin kahon Afirka, da yankin manyan tafkunan Afirka, da yankin Sahel da wasu bangarori na arewacin Afirka.

Alkaluma daga cibiyar nazari da binciken ayyukan ta’addanci ta kungiyar AU, sun nuna cewa, an samu matukar karuwar yawa, da kuma illar ayyukan ta’addanci a shekarar 2023 da ta gabata.  (Saminu Alhassan)