logo

HAUSA

Biden ya lashi takobin gaggauta samarwa Ukraine karin makamai

2024-04-23 10:33:55 CMG Hausa

Shugaban Amurka Joe Biden, ya shaidawa takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky cewa, nan ba da jimawa ba, gwamnatinsa za ta samar da karin makamai ga Ukraine, da zarar majalisar dokokin kasar ta zartas da kudurin dake da alaka da batun.

Fadar White House ta ruwaito cewa, da suke tattaunawa ta wayar tarho a jiya Litinin, shugaba Biden ya ce gwamnatinsa za ta gaggauta samar da sabbin shirye-shiryen tallafin tsaro domin cimma bukatun Ukraine na gaggawa a fagen daga da ma bukatunta na tsaron sararin samaniya, da zarar majalisar dattawan kasar ta zartas da kudurin, kana ya rattaba masa hannu domin zama doka.

Joe Biden na wannan furuci ne dangane da tallafin dala biliyan 61 ga Ukraine da majalisar wakilan kasar ta amince da shi a ranar Asabar. A wannan mako ne kuma majalisar dattawan kasar za ta kada kuri’a kan kudurin wanda ya kunshi tallafin kudi ga wasu kasashe, a matsayin wani karin kudurin kasafin kudin tsaro na kasa, wanda shugaba Biden ya lashi takobin rattabawa hannu da zarar ya isa teburinsa. (Fa’iza Mustapha)