logo

HAUSA

Sin da kasashen Afirka na kokarin inganta hadin gwiwar kwararru a fannoni daban daban

2024-04-23 16:00:35 CMG Hausa

A shekarun nan, a karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC a takaice, hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka na kara zurfi a fannin horar da kwararru. A cikin shirinmu na yau, bari mu je wurin samar da horon sana’o’i na Luban dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha, da kwalejin Confucius ta jami’ar Dar es Salaam dake kasar Tanzaniya, don ganin nasarorin da aka samu ta hanyar hadin gwiwar kwararru tsakanin Sin da kasashen Afirka.