logo

HAUSA

Shugaba Xi Ya Jagoranci Taron Karawa Juna Sani Game Da Bunkasa Ci Gaban Yankin Yammacin Kasar

2024-04-23 21:10:11 CMG Hausa

Da yammacin yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci wani taron karawa juna sani a birnin Chongqing, game da bunkasa ci gaban yankin yammacin kasar Sin a sabon zamani.

Cikin muhimmin jawabin da ya gabatar yayin zaman, shugaba Xi ya jaddada cewa, yankin yammacin kasar Sin na taka muhimmiyar rawa, wajen yin gyare-gyare a kasar da samun ci gaba da kuma daidaito.

Ya ce, wajibi ne a aiwatar da manufofi, da matakan kwamitin kolin JKS, ta fuskar ingiza ci gaban yankin na yammacin Sin, kana a kara kafa wani sabon salo na kare kai, da kara bude kofa ga ketare, da samun ci gaba mai inganci, da bunkasa daukacin karfi, da kwarewar bunkasa kai mai dorewa na yankin, a kuma kara azamar bude sabon babi na bunkasa yankin na yammacin Sin, karkashin burin zamanantarwa irin na kasar Sin.   (Saminu Alhassan)